Uwargidan shugaban Kasa ta bayyana wa taron matan Najeriya cewa kasar nan ta fada cikin matsalolin da take ciki ne saboda mazan Najeriya sun kyale wasu mutane biyu zuwa uku kacal sun kanannade mijin ta wato shugaba Muhammadu Buhari suna cin karen su babu babbaka.
Aisha ta ce mutane miliyan 15.5 ne suka zabi shugaba Buhari amma sun kyale shi sai juya shi ake yi sannan kuma ma mutane biyu ne kacal ke yin haka kuma an zuba musu ido babu wanda yake iya ce musu kala.
” Irin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu a yanzu da kyar duk a dalilin wadannan mutane ne. Da ace ba su tare da Buhari da ci gabar ya fi haka.
” Sannan kuma maza na kallo babu mai iya cewa kala a kai. Babu hadin kai kwata-kwata. Maimakon manyan ‘yan siyasa su fito su koka kan haka, A’a sun koma ne sai bin wadannan mutane suke yi suna maula suna goge musu takalma.”
Aisha ta jaddada cewa wannan gwamnati na mijin ta babu hadin kai ko na miskala zarratin. Wadannan mutane na yadda suka dama a gwamnati sannan an zuba musu ido mijin ta, wato shugaba Buhari na ta wahala maza sun kwanta shiru abin su.
Ta ce za a samu ci gaba ne kawai idan kowa ya zo aka hada kai domin kasa baki daya.
Idan ba a manta ba Aisha Buhari ta taba yi wa Buhari gargadin cewa ko ita da kanta ba za ta mara masa baya ba idan bai canja salon mulkin sa ba sannan ya yi watsi da wadannan da ke zagaye da shi suna hana shi aiki.
Da alamar har yanzu dai Uwargida Aisha ba ta jin dadin abubuwan da ke faruwa a gwamnati duk da cewa ta dawo daga baya bayan nan ta ce tana tare da Buhari a zabe mai zuwa.
Premiumtimeshausa.
No comments