Kannywood A baya mun yi soyayya da Adam A. Zango, sai dai yanzu mutunci ne kawai tsakaninmu – Nafisa Abdullahi

Share:
- Nafisa Abdullahi ta bayyana alakar da ke tsakanita da jarumi Adam A. Zango a yanzu


- Tace a baya sun yi soyayya da shi, sai dai yanzu mutunci ne kawai tsakaninsu, amma ba soyayya ba

- Jarumar ta kuma ce yanzu ta dauki Zango a matsayin abokin aiki amma ba masoyi ba




Shahararriyar jarumar na ta masana’antar shirya fina-finan Hausa wato Kannywood Nafisa Abdullahi ta bayyana matsayar soyayyarta da jarumi Adam A. Zango, a cewarta a baya sun yi soyayya da shi, sai dai yanzu mutunci ne kawai tsakaninsu, amma ba soyayya ba.

A shekarun baya an yi tunanin Nafisa Abdullahi da Adam za su yi aure duba ga yadda suka fito karara suka nuna suna matukar kaunar juna.



Amma Jarumar ta ce yanzu tsawon shekara biyar ba su tare. Ta ce kamar yadda Allah Ya hada su kuma Ya raba.

Nafisa ta ce: "Ba sai na fito na fara bayanin an yi kaza ko kaza ba, zama ne ya zo karshe muka rabu," in ji Nafisa bayan an tambaye ta dalilin rabuwarsu.

A baya mun fi ayyuka tare kuma an fi ganinmu tare amma yanzu ba mu cika haduwa da juna ba sosai saboda ban cika fitowa a fina-finai ba."

Jarumar ta ce yanzu ta dauki Zango a matsayin abokin aiki amma ba soyayya tsakaninsu.

Ta ce ba su cika haduwa da shi ba a yanzu."Ba mu da wata matsala ta rashin jituwa da juna tsakani na da shi."

No comments