Rikici A Kan Budurwa Ya Janyo An Datse Hannun Wani Matashi A Yola

Share:

Rundunar 'yan-sandan jihar Adamawa ta bayar da tabbacin damke wani mutum mai suna Abubakar Yahaya sakamakon datse wa wani mutum mai suna Muhammad Jafar hannun hagunsa yayin fada a kan budurwa.

Kakakin rundunar 'yan-sandan, SP Othman Abubakar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya.

Abubakar, wanda ake wa lakabin Asia, mazaunin mahadar Geriyo, Jimeta, da kuma Muhammad mazaunin Demsawo, itama ta Jimeta, sun samu kansu a cikin fada mai tsanani wanda ya hada har da abokanansu a kan wata yarinya mai suna Maryam Boni. A yayin da suke kafsa fadan ne Abubakar ya sanya adda ya datse hannun Muhammad na hagu.

A dangane da jawabin 'yan-sanda, fadan ya samo asali ne yayin da Maryam, wacce take budurwar Abubakar, ta yanke shawarar datse soyayyar tasu da Abubakar inda ta koma gurin Muhammad. Hakan shi ya sanya su Abubakar suka yanke hukuncin kai wa Muhammad farmaki domin zabar shi da ta yi a matsayin sabon masoyi.

'Yan sandan sun ce sun yi gaggawar shawo kan rikicin inda suka damke Abubakar, shi kuma Muhammad aka garzaya da shi asibiti.

Kakakin rundunar 'yan sandan, Othman Abubakar, ya yi holin Abubakar da sauran wasu masu laifi daban-daban a shelkwatar 'yan sandan da ke Yola.

Sarauniya.

No comments